Ýar kunar bakin wake ta hallaka masu bauta 10 a masallacin Maiduguri

Ýar kunar bakin wake ta hallaka masu bauta 10 a masallacin Maiduguri

Wata ‘yar kunar bakin wake ta tayar da bam wanda ya kashe masu bauta 10 da suka zo yin sallah a wani masallaci a Maiduguri, jihar Borno, a safiyar ranar Litinin 17 ga watan Yuli.

Harin bam din shine sabon hari cikin hare-haren da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai tun bayan sakin wasu kwamandojin kungiyar inda aka canja su da wasu ‘yan matan Chibok da aka sace, jaridar Cable ta ruwaito.

NAIJ.com ta tuna cewa akalla mutane 11 ne suka mutu a wani hare-hare biyu da ya afku a daren ranar Talata, 11 ga watan Yuli.

Ýar kunar bakin wake ta hallaka masu bauta 10 a masallacin Maiduguri

Ýar kunar bakin wake ta hallaka masu bauta 10 a masallacin Maiduguri

Wata majiyar tsaro abun dogaro, wacce ta nemi a boye sunanta, ta fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa harin na farko da biyu sun afku ne da misalin karfe 9.45 na dare a Mulaikalmari, wasu kilomita shidda daga Maiduguri.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya aika sako ga mutanen Jihar Sokoto

Majiyar ta bayyana mutane takwas, wanda suka hada da ‘yan kunar bakin waken suka mutu a harin.

Mutane uku sun kuma mutuwa sannan wasu biyar suka jikkata a tashin bam na uku da hudu, wanda ya afku kimanin mintuna 20 bayan na farkon a yankin Polo-Sabon Gari dake Maiduguri, a cewar majiyar, wacce ta ce ta taimaka gurin harhada wadanda abun ya cika da su a gurin da tashin bam din ya afku.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel