Wani ya daganta rushewar gadan hanyar Mokwa ga shugaban majalisar dattawa

Wani ya daganta rushewar gadan hanyar Mokwa ga shugaban majalisar dattawa

- Wani mutum soki lamirin shugaban majalisar dattawa kan rushewar kadan Talabu a Mokwa

- Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya za ta gyara gadan nan da nan

- Wannan hanyar ce kadai ta hada yankin areawa da kudu maso yammacin kasar

Wani mutum mai suna George Udom ya kalubalanci shugaban majalisar dattawa, sanata Bukola Saraki inda ya rubuta a shanfisa ta Facebook cewa: “ Ku gani wannan ne kawai hanyar da ta hada garin Saraki zuwa Mokwa, da Jebba da kuma Ilorin birnin jihar Kwara. Amma a waye gari zai ga hanyar ta rabu biyu”.

“Duk da haka, maimakin wannan ya janyo hankalin sa ta yadda za a gyara hanyar zai gashi yana ta barnar miliyoyin kudi don ya kalubalanci gwamnatin shugaba Buhari”. A cewar Udom.

Idan baku manta ba, NAIJ.com ta ruwaito cewa a makon da ta gabata mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari za ta gyara gadar Talabu da ta rushe a karamar hukumar Mokwa wanda kuma ta hada yankin areawa da kudu maso yammacin kasar nan ba da jumawa ba.

Wani ya daganta rushewar gadan hanyar Mokwa ga shugaban majalisar dattawa

Gadar Talabu da ta rushe a karamar hukumar Mokwa

KU KARANTA: Gwamnatin Shugaba Buhari ta taro fadin da ya fi karfin ta

Amma abin mamaki a nan shine ta yadda wannan mutum ya daganta rushewar gada ga shugaban majalisar dattawan, saboda karamar hukumar Mokwa ta kasance a jihar Neja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel