Gwamnatin Shugaba Buhari ta taro fadin da ya fi karfin ta

Gwamnatin Shugaba Buhari ta taro fadin da ya fi karfin ta

- Gwamnatin Tarayya ta tabo tsuliyar dodo game da haramta waka a waje

- Jama’a da dama sun soki wannan doka su kace sam ba za ta sabu ba

- Tuni ma fitattun Mawakan Najeriya su kace Gwamnati kasar tayi kadan

Gwamnati Shugaban kasa Buhari na nema ta dauko abin da ya fi karfin ta game da haramtawa Mawakan kasar fita waje domin yin bidiyo waka kamar yadda da dama su ka saba.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta taro fadin da ya fi karfin ta

Hoton Miistan labarai da al'adu na Gwamnatin Buhari

Mun samu labari cewa Jama’a da dama sun soki wannan doka ta Gwamnatin Tarayya. Daya daga cikin masu sukar a kafafen zamani yace idan har da gaske ake yi sai Gwamnati ta haramta fita waje ganin Likita da kuma zuwa karatu.

KU KARANTA: Atiku yayi kira a gyara kasar nan ta garambawul

Gwamnatin Shugaba Buhari ta taro fadin da ya fi karfin ta

Manyan Mawakan Najeriya Davido da Wizkid

Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ne yace dole a hana wannan don Najeriya ta cigaba. Ku na sane cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Landan inda yake jinyar rashin lafiya. Haka ma dai ‘ya ‘yan sa da dama a Landan din su ke karatu ba a nan gida ba.

Tun ma dai bayan tafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari har yau ba a ga hoton sa ba illa dai wani sakon da ya aiko lokacin bikin karamar Sallah ga Musulman kasar wanda hakan ya fara jawo magana.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ambaliyar ruwa ya addabi Garin Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel