Wa ta makarkashiya ne ake shirya kuma; wasu ‘yan majalisa sun ziyarci Tinubu

Wa ta makarkashiya ne ake shirya kuma; wasu ‘yan majalisa sun ziyarci Tinubu

- Wasu ‘yan majalisar tarayya sun ziyarci jigon dan siyasan nan sanata Bola Ahmed Tinubu a Legas

- Tinubu ya bukaci ‘yan majalisar da sanya dokokin da zai ciyar da kasar gaba

- Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce sun ziyarci Tinubu don su girmama masa a matsayin tsohon sanata

Shugaban jama'iyyar mai mulki ta APC, Bola Tinubu ya shawarci 'yan majalisar tarayya cewa su yi dokokin da zai taimaka wajen inganta ci gaban kasar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Tinubu ya yi kiran ne a lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya jagoranci kwamitin majalisar dattijai da na wakilai kan nazari na kundin tsarin mulkin 1999 a lokacin da suka ziyarce shi a gidansa da ke Legas a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli.

Tinubu ya yaba wa kokarin 'yan majalisar a kan hanyoyi ta yadda za a gyara kundin tsarin mulkin kasar.

Wani makarkashiya ne ake shirya kuma; wasu ‘yan majalisa sun ziyarci Tinubu

Bola Tinubu da 'yan majalisar tarayyar Najeriya a lokacin da suka ziyarci Tinubu a gidansa

"Na roke ku da ku ci gaba da yin aiki ta yadda za a samu hadin kan al'ummar kasar. Na yi alkawari ba da gudunmawa na a duk lokacin da aka bukaci wani abu ko shawarwari ta yanda kasar zai ta ci gaba”. A cewar Tinubu.

KU KARANTA: Bayan Osinbajo ka ji wadanda su ka ga Buhari a Landan

Da yake jawabi a baya, sanata Ekweremadu ya ce sun ziyarci jigon dan siyasan ne don su girmama masa a matsayin wani shahararren shugaba da kuma wani tsohon sanata. Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana shi a matsayin mutum mai basira.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel