Dole a saki Evans don kuwa 'Yan Sanda ba su kama shi da laifin komai ba - Inji Lauyan Sa

Dole a saki Evans don kuwa 'Yan Sanda ba su kama shi da laifin komai ba - Inji Lauyan Sa

- Kasurgumin mai garkuwa da mutane Evans yanzu haka yana hannun Hukuma

- Lauyan sa yace ya kamata a sake sa don ba a kama sa da laifi ba a shari’a

- 'Yan Sanda sun yi nasarar damke gawurtaccen mai laifin kwanakin baya

Rundunar 'Yan Sanda tayi nasarar damke gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kasar nan watau Evans inda ake cigaba da bincike kafin a maka sa a gaban kuliya.

Dole a saki Evans don kuwa 'Yan Sanda ba su kama shi da laifin komai ba - Inji Lauyan Sa

Hoton Evans da kuma Lauyan Sa Obasa

Sai dai Lauyan da ke kare wannan mutumi da ake zargi da sace mutane da dama yayi garkuwa da su watau Olukoya Ogungbeje yace babu wata shaida da ta nuna cewa Evans din mai laifi ne a gaban Hukuma don haka ya kamata a sake sa.

KU KARANTA: An damke wasu dauke da kan mutum

Dole a saki Evans don kuwa 'Yan Sanda ba su kama shi da laifin komai ba - Inji Lauyan Sa

Hoton Kasurgumin mai garkuwa da mutane a hannun 'Yan Sanda

Wasu ma dai na tsoro ko an kashe wannan ta'aliki ganin yadda aka ji tsit ba a jin motsin sa gaba daya. Fiye da wata guda kenan da kana Evans, Lauyan yace akwai matsala cigaba da tsare Evans din.

Kun ji cewa dn damke masu satar Jama'a su na garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa kaduna kwanan nan. Dama Sufeta Janar na 'Yan Sanda ya sa kafar wando tsakanin sa da masu satar Jama'ar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin da gaske Evans ya bace daga hannun 'Yan Sanda

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel