Dasuki yayi magana daga kurkuku, yayi bayanai kan Boko Haram da ma zaben 2015

Dasuki yayi magana daga kurkuku, yayi bayanai kan Boko Haram da ma zaben 2015

- A shekarar 2015 ne aka garkame Sambo Dasuki, tsohon shugaban hukumar NSA

- An bankado badakala mafi girma a tarihin kasar nan karkashin sa

- Yace kokarin da suka yi na yaki da Boko Haram ne ya kai ga nasarar wannan gwamnati

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai ya karbi ragamar mulki a 2015, kuma yaci gaba da aikida shugaban NSA na wancan lokacin Sambo Dasuki, sai dai bayan watanni, an kame Sambo Dasukin an kulle bisa laifuka da ake tuhumanrsa dasu.

Laifukan dai sun hada da almundahana da ajje makamai a cikin gida, da sace makudan kudaden gwamnati da ma kokarin da yayi a baya na dage zaben 2015 da makonni, saboda wai matsalolin tsaro.

Dasuki yayi magana daga kurkuku, yayi bayanai kan Boko Haram da ma zaben 2015

Dasuki yayi magana daga kurkuku, yayi bayanai kan Boko Haram da ma zaben 2015

Daga kulle dai Sambo Dassukin yayi magana, wanda aka jima ba'a gani ba tun bayan rasuwar mahaifinsa, Sarkin Musulmi Dasuki. A littafin da Yusha'u Adamu ke rubutawa mai shafuka 308, mai taken 'Yaki a Boko Haram ta sashen labaru: Taunawa da shugaban leken asiri'.

A cikin littafin dai, Sambo Dasuki yace, kokarin gwamnatinsu ta waccan lokacin, karkashin Goodluck Jonathan ne ya saka suka fatattaki 'yan Boko Haram wadanda suka mamaye babban yanki a Najeriya, inda hakan ya baiwa 'yan Najeriya damar shiga da dangwala kuri'unsu a zabukan 2015 din.

DUBA WANNAN: Kamanceceniyar rashin lafiyar Buhari da Yaraduwa

A cewarsa, ba don kokarin su ba, da baza ayi zabuka a wannan shekara ba, kuma ma dai sun yi shiri na wayar wa da kamammun mayakan Boko Haram, da ma wadanda suka mika wuya, domin wanke musu mugun tunani da koya musu sake zama cikin al'umma, ba tare da amfani da makami ba, wanda wannan gwamnati ke amani da shi, da suna 'Operation Safe Corridor'.

Har yanzu dai ba'a gama shari'ar Sambo Dasuki ba, ba kuma a gama samo kudade da ya rabar ko ya batar ba, yayin zamansa a gwamnati.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel