A shirye nake in je kurkuku - Tsohuwar minista Diezani

A shirye nake in je kurkuku - Tsohuwar minista Diezani

-Masu bincike sun samu sakon murya wanda sukace tsohuwar ministan ta amsa cewa ta taimaka ma wasu mutane samun kudi mai dimbin yawa

-Sakon muryar dai a yanzu yana hannun bangaren shari’a na kasar Amurka a matsayin sheda a karar da aka shigar

-Bana shakkan zuwa kurkuku, inji Alison Madueke

Tsohuwar minstan man-fetur, Diezani Alison Madueke wace ake bincika akan laifufuka da suka shafi safaran kudi wanda yawan su ya kai biliyoyin dalla a Najeriya, Igila har ma da kasar Amurka tayi barazanar tona abokanan huldan ta, wato Kola Aluko da Jide Omokore.

Tace bayan yin bayanni akan haramtaciyyar cinikayya da suka yi, a shirye take da ta tafi kurkuku tare da wadanda sukayi huldan tare.

A shirye nake in je kurkuku - Tsohuwar ministan Diezani

A shirye nake in je kurkuku - Tsohuwar ministan Diezani

Wannan kakausan magana da tsohuwar ministan tayi an same shi daga wata daukar murya da akayi na hira ta su wanda masu bincike akan laifufukan da ake zargin nata dashi suka zakwulo.

KUMA KU KARANTA: Dasuki yayi magana daga kurkuku, yayi bayanai kan Boko Haram da ma zaben 2015 Read

Sauran bayanin da ke cikin hirar an mika shi da zuga ga bangaren binciken sharia da ke kasar Amurka a matsayin hujja a wata kara da aka shigar inda ake neman tsohuwar ministan da abokan laifin nata su biya dalla miliyan 144 a matsayin kudin da suka karkatar daga aljihun gwamnati

Mutanen uku wato Uwargida Alison-Madueke, Mr Aluko da Mr. Omokore duk suna cikin mutanen da ake zargi a cikin wata kara da aka shigar. Karar da aka shigar ya nuna yadda mutane wasu mutane uku suka taimaka ma tsohuwar ministan wajen satan kudi wanda daga baya sukayi amfani da kudin wajen siyan kadarori a Ingila da Amurka, inda ita kuma tsohuwar ministan ta saka musu da basu kwangila mai kauri da hannun kamfanonin su masu suna Atlantic Energy Drilling Concept Ltd (AEDC) da kuma Atlantic Energy Brass Development Ltd (AEBD), duka kampanonin mallakar Mr Omokere ne.

A wata hirar da tsohuwar ministan tayi da Mr Aluko wadda ministan tayi a watan Mayu na shekarar 2014, anji ministan karara ta ambaci cewa ta taimaka ma abokanan huldan nata wurin samun kudade da suka haura biliyoyin naira.

A wata hirar kuma ta nuna bacin ranta a yadda abokanan huldan nata suke ta siyan kayan alatu masu tsada wanda tace hakan ne ya sama jami’an tsaro suka fara bincike a kansu. Ta nuna baccin ranta karara akan wata jirgin ruwa na shakatawa da Mr Aluko ya siya mai suna Galatical Star a kan kudi $80,000,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel