Cikin fatara na baro kurkuku a 1998 - Tsohon Shugaba Obasanjo

Cikin fatara na baro kurkuku a 1998 - Tsohon Shugaba Obasanjo

- Obasanjo ya ce a talauce ya baro kurkukun Yola a 1998

- Abacha dai ya daure OBJ daurin rai da rai a 1995

- An zabi shugaba Obasanjo a 1999

A shekarar 1998 ne dai Janar Abacha ya mutu, kuma mako daya kacal bayan nan Janar Abdussalami Abubakar ya sako Janar Obasanjo.

Obasanjo yace a sa'ilin da ya baro kurkuku bashi da ko asi, don haka ko kudin makarantar yara baya iya biya, sai dai zuwansa Amurka ya samo makudan kudade daga abokai.

Cikin fatara na baro kurkuku a 1998 - Tsohon ShugabaObasanjo

Cikin fatara na baro kurkuku a 1998 - Tsohon ShugabaObasanjo

A fadin Obasanjo, bayan baro kurkuku, sai kawai yaga motoci na alfarma sun zo daukar sa, inda yace yayi mamaki matuka. A tafiyarsa Amurka ma, jirgin da Abacha ke hawa aka bashi, inda ya kai ziyara ga abokai kamar su Jimmi Carter da Ted Turner mai kamfanin CNN, kari da ma Ford, mai kamfanin motoci.

DUBA WANNAN: Zan iya tara makudan kudade daga kishingide a lambu na - Sarkin Kano

Yace a wannan tafiya, sai gashi ya tashi da dala $150,000, wadda yayi amfani da ita wajen biyan kudin makarantar yara da ke karatu a Amurkar, sannan ya dawo gida.

Obasanjo, yace rahamar Yesu ce take bibiyarsa kuma yayi wa Ikilisiyar aiki tun yana kurkuku, inda har kasurgumin dan fashi ya shiryar zuwa ga hanyar Masihanci, wanda yace yanzu haka ya zaman faston coci.

A yanzu dai gonar shugaba Obasanjo ta tumbatsa inda ta ke da jari na biliyoyin kudi, wadda ya habaka lokacin yana mulki a 1999-2007.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel