An yi ram da wadanda su ka fitini da Jama'a a hanyar Kaduna zuwa Abuja

An yi ram da wadanda su ka fitini da Jama'a a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun shiga hannu

- Sufeta Janar na 'Yan Sanda ya sa kafar wando tsakanin sa da masu laifin

- 'Yan Sanda sun damke mutane kusan 8 da su ka matsawa Jama'a

An damke masu satar Jama'a su na garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa kaduna kwanan nan. Dama Sufeta Janar na 'Yan Sanda ya sa kafar wando tsakanin sa da masu satar Jama'ar.

An yi ram da wadanda su ka fitini da Jama'a a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Hotunan wasu masu garkuwa da mutane daga Premium Times

Dama a Watan jiya Rundunar 'Yan Sanda ta karo 'Yan Sanda 600 domin takawa masu satar Jama'ar burki wanda yanzu an yi nasarar damke mutane 8 da makamai wadanda sun ma amsa laifin su.

KU KARANTA: An bankado wata badakala a Jami'ar Arewa

Kadan daga wadanda aka kama da makamai su ne:

1. Ibrahim Gurgu, Gwagwada

2. Abdulaziz Idris, Kankara

3. Shuaibu Ibrahim, Kankara

4. Ibrahim Isiaku, Gwagwada

5. Usman Datti, Gwagwada

6. Kabiru Musa, Dandume

7. Haruna Umar, Dandume

Kwanaki ‘Yan Sanda kuma su ka kama wata Budurwa mai shekara 20 ta bada kyautar 'Dan ta inda aka ba ta rabin buhun shinkafa da kuma kudi har N200,000 da ma wasu kayan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da fafutukar neman Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel