Wani babban fasto ya tofa albarkacin bakinsa kan hadin kan kasa, karanta

Wani babban fasto ya tofa albarkacin bakinsa kan hadin kan kasa, karanta

- Bishop na Katolika Diocese na Sakkwato ya ce hadin kan kasar Najeriya abu ne da ya zama dole ga ‘yan kasar gaba daya

- Kukah ya bukaci masu ruwa da tsaki a kasar su yi aiki don tabbatar da zaman lafiyar kasar

- Kukah ya kuma ce damokaradiyya zai samu karfafawa ne kawai idan aka ba mutane yancin bayyana damuwarsu ba tare da takura ba

Babban Bishop na Katolika Diocese na Sakkwato, Rev. Matiyu Kukah, ya ce hadin kan kasar Najeriya abu ne da ya zama dole ga ‘yan kasar ida ana bukatar kasar ta ci gaba.

Kukah ya kuma bukaci ‘yan Najeriya baki daya da su hada hannu don a cimma wannan manufar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Kukah ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli 2017 a birnin tarayya Abuja a wata taron tattauna na kasa shirin da wani kungiyar ‘’ Savannah Centre for Diplomacy Democracy and Development’’ ta shirya.

Kukah, a lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa ga yunkurin wasu kungiyoyin yankunar kasar, ya ce damokaradiyya zai samu karfafawa ne kawai idan mutane na da damar bayyana damuwarsu ba tare da wani takura ba.

Wani babban fasto ya tofa albarkacin bakinsa kan hadin kan kasa, karanta

Babban Bishop na Katolika Diocese na Sakkwato, Rev. Matiyu Kukah

KU KARANTA: Furucin matasan Arewa yayi dai-dai, Karen bana ne maganin zomon bana - wani babban masani

Ya ce: "Ba zai yu mu kwace wani yankin kasar daga ‘yan ta’adda Boko Haram kuma mu mika wani yanki kuma ga wasu. Dukan mu ‘yan Najeriya ne kuma Najeriya za ta ci gaba da zama a matsayin mazauni daya”.

Ya ce kalubalen da ke gaban mu yanzu haka shine yadda za a yi Najeriya ta ci gaba, ya kara da cewa duk masu ruwa da tsaki a kasar su yi aiki don tabbatar da hakan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel