Fadar Aso Rock ta yi wayam, Osinbanjo na cikin hadari - Manzo Ayodele

Fadar Aso Rock ta yi wayam, Osinbanjo na cikin hadari - Manzo Ayodele

-Osinbanjo yana gwagwarmaya ta makiya wanda ke son ganin bayansa

-Nan gaba kadan masu yin hassada ga Osinbanjo zasu bayyana

-A yanzu PDP na bukatar gyara, Makarfi zai iya farfado da jami’iyyar

Shahararen malamin addini mai suna Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya bayyana cewa ran mukadashin shugaban kasa Osinbanjo tana cikin hadari. Ya kuma bayanna cewa mukadashin shugaban kasa yana gwagwarmaya da wasu manyan kasar da ke kusa da shugaba Buhari wanda ke kokarin kauda Osinbanjo daga kujerar mulki.

Manzo Ayodele ya ci gaba da cewa kada jami’iyyar PDP tayi tsamanin nasarar da ta samu a zaben jihar Ogun yana nufin jami’iyyar ta gama farfadowa ne.

'Fadar Aso Rock ta yi wayam, Osinbajo na cikin hadari' - Manzo Ayodele

'Fadar Aso Rock ta yi wayam, Osinbajo na cikin hadari' - Manzo Ayodele

Amma, yace hukuncin da kotun koli da ke Abuja ta zartar wadda ta ba Senata Makarfi shugabancin jami’iyyar alama ce da ke nuna jami’iyyar ta fara farfadowa.

DUBA WANNAN: Arewa bata isa ta hana ni magana ba, inji FFK

Primate Ayodele ya shaida wa jaridar Sun cewa, “Ran Osinbanjo yana cikin hadari amma Ubangiji sai kare shi.

Daga baya asirin masu nuffin sa da shari zai tonu.

“Akwai abubuwa da yawa da baza mu iya gani ba yanzu; mukadashin shugaban kasa yana fama da makiya sosai. A yanzu villa wayam take.

“A halin yanzu jami’iyyar PDP na bukatan garanbawul. Makarfi sai iya farfado da jami’iyyar amma idan basu tsayar da dan takaran da ya dace ba a zaben 2019, akwai yiwuwar baza suyi nasara ba.

“Jami’iyyar APC zata tsinci kanta a cikin tsaka mai wuya yanzu da Makarfi ya zama tabbatacen shugaban PDP sai dai idan jami’iyyar APC tayi gyara cikin kuma ta sake dabara.

“Idan jami’iyyar APC na son su cigaba da mulkin kasan nan, ya zama dole su yi gyara kuma su hada kansu a jami’iyyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel