Shugaba Buhari na duba yiwuwar dawowa aiki cikin makon karshe na wannan watan bayan jinyar watanni 7

Shugaba Buhari na duba yiwuwar dawowa aiki cikin makon karshe na wannan watan bayan jinyar watanni 7

- Shugaba Buhari na duson dawowa gida Najeriya, bayan samun sauki

- An gano sabbin hotunan shugaban a birnin Landan

- Ya shafe wata da watanni a bana ba ya Najeriya

A cikin kwanakin nan ne dai ake sa ran ganin dawowar shugaba Muhammadu Buhari tun bayan da ya dauki hutu ya tai jinya asibiti a Ingila a watan Mayu.

Ziyarar mukaddashinsa Faresa Yemi Osinbajo ta nuna lallai shugaban baya asibiti kuma, domin yana zama ne a wani gidan Alfarma a wajen birnin Landan, inda yake kara murmure wa, gida na Najeriya wanda ake wa lakabi da Abuja House.

Shugaba Buhari na duba yiwuwar dawowa Najeriya

Shugaba Buhari na duba yiwuwar dawowa Najeriya

A binciken mu dai, NAIJ.COM ta gano muku cewa shugaba Buhari na duba yiwuwar komo wa gida domin kawar da yamadidi da ake kan batun lafiyar tasa, dama komawa bakin aiki domin kaarasa ayyukan da yayi wa talakawa alkawari.

A lokacin da baya nan dai, shugaban ya sami ziyarar wasu manyan gwamnati kebabbu, inda suka tabbatar ya ara samun sauki, kuma yana shirin dawowa gida.

Ana sa ran dai shugaban zai hakura da neman takara a zabuka masu zuwa saboda rashin koshin lafiya da yanayi na tsufa.

DUBA WANNAN: Arewa bata isa ta saka ni inyi shiru ba'

A yanzu dai, daga majiya mai karfi shugaba Buhari na iya dawowa cikin wannan wata na Yuli, kamar nan da makonni biyu kenan, kuma idan yazo, akwai muhimman abubuwa da zayyi na sauye-sauye da nade-nade a zangon karshe na mulkin nasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel