Kwatankwacin yawan kudaden kasafin kudin bana 'yan Najeriya suka kashe a sayen kayan kasashen waje a 2015

Kwatankwacin yawan kudaden kasafin kudin bana 'yan Najeriya suka kashe a sayen kayan kasashen waje a 2015

-Aisha Abubakar ta koka kan dimbin kudaden da yan Najeriya ke kashe wa wajen sayan kayan kasashen waje

-An gudanar da taro domin nemo hanyoyin da za’a rage dogaro da kayayakin kasashen waje

-Osinbanjo ya saka hannu a wata takarda da zata tabattar kashi 40 na kayayakin da ma’aikatun gwamnati ke amfani da su ba na kasashen waje bane

A jiya ne karamar ministan kasuwanci da saka jari, Uwargida Aisha Abubakar ta bayyana cewa yan Najeriya sun kashe naira tiriliyan 6.7 wajen sayen abinci da kayan gida daga kasashen waje a shekarar 2015.

Ta fadi wannan Magana ne a garin Kano a wani taro da aka shirya na masu hannu a cikin harkan kasuwanci da saka jari, manufan taron shine a nemo hanyoyi da za’a rage siyo kaya daga kasashen waje a koma siyan kayan mu na gida Najeriya. An tsara taron ne da hadin gwiwan ma’aikatan yada labarai da al’adu na kasa.

Kwatankwacin yawan kudaden kasafin kudin bana 'yan Najeriya suka kashe a sayen kayan kasashen waje a 2015

Kwatankwacin yawan kudaden kasafin kudin bana 'yan Najeriya suka kashe a sayen kayan kasashen waje a 2015

Aisha tace baza mu amince da dumbin kudin da ake kasha wa wajen siyo kaya daga kasashen waje, ya kamata a nemo hanyoyin wayar da kan yan Najeriya domin su rika siyan kayan gida Najeriya.

DUBA WANNAN: Arewa bata isa ta saka ni inyi shiru ba, su harbo in harba ne - Fani-Kayode

Ta ce: “A shekarar 2015 kawai, Najeriya ta kasha sama da naira tiriliyan 6.7 akan siyo kaya daga kasashen waje wanda zamu iya samar dasu a nan gida Najeriya.

Har illa yau, rahotanni sun ce an kashe naira tiriliyan 1.09 akan abinci da abin sha; naira triliyan 1.5 akan spaya parts; N1123.01 biliyan wajen sayo takalma da tufafi da kuma N399 biliyan akan siyo kayayakin aiki na gida. Ina ma da duk wannan kudin mun kashe shi wajen sayan kayan mu na gida.”

Karamar mininstan tace gwamnati baza tayi kasa a gwiwa ba wajen bada gudunmawa domin mutane su rika sayan kayayakin mu na gida Najeriya ta hannun hukumomi da ma’aikatun gwamnatin da alhakin ya rataya a kansu. Wannan ne yasa mukadashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya sa hannu a wata takarda wanda zata tabbatar kashi 40 na cikin kayayankin da ma’aikatun gwamnati ke amfani dashi ana yin su ne a gida Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel