Hukumar sojin saman Najeriya NAF ta yaye dalibai 298

Hukumar sojin saman Najeriya NAF ta yaye dalibai 298

- Hukumar sojin saman Najeriya ta yaye wasu dalibai 298 bayan wata horor na musamman da aka musu

- Akwai wasu jami’an sojan sama da aka horas domin su horor da dalibai kan dabarun yaki na musamman

- Tawagar BMATT 66 suka kasance a shirin

Hukumar sojin saman Najeriya ta yaye wasu dalibai 298 wadanda tawagar sojin horaswa ta kasar Biritaniya (BMATT) suka yi musu horon makamai na musamman. Tawagar ta kuma yiwa wasu jami’an sojin sama na Najeriya horo na musamman don taimaka musu horar da wasu dalibai NAF a kan dabarun yaki.

Da yake jawabi a bikin, babban bako kuma babban hafsan sojan sama (CAS), Air Marshal Sadique Abubakar, ya nanata kudurin na NAF kan yadda jami’an za su samu damar ci gaba. Abubakar ya lura da cewa wannan horor na musamman ya zama dole ga dalibai kasancewa kalubalen da kasar ke fuskanta a wasu yakunan kasar yanzu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Abubakar ya bukaci dalibai da su yi amfani da horor don inganta rayuwar al’ummar kasar. Ya tabbatar cewa rundunar za ta ci gaba da irin wannan horor da kuma inganta duk abin da ya shafi rayuwar dalibai. Air Marshal Abubakar ya bukaci dalibai cewa su zama masu bin doka da oda da kuma kare hakkin dan adam a cikin aikinsu.

Hukumar sojin saman Najeriya NAF ta yaye dalibai 298

Dalibai na sojan sama na Najeriya da tawagar sojin horaswa ta kasar Biritaniya (BMATT)

A cikin jawabinsu, shugabanin kwamitin majalisar dattawa kan sojan sama, wanda sanata Aliyu Wakili ya wakilta da kuma na kwamitin majalisar wakilai, Hon. Samson Okwu sun yaba jagorancin shugabanin kan ci gaban NAF a 'yan lokutan. ‘Yan majalisar sun kuma yi alkawarin ci gaba wajen ba rundunar goyon baya da ta bukata.

KU KARANTA: Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

Tawagar sojin horaswa na musamman ta kasar Biritaniya (BMATT) 66 suka kasance a shirin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel