Obasanjo ya nesanta kansa da sunansa na kirista, ya ce kul aka sake kiransa da Matthew

Obasanjo ya nesanta kansa da sunansa na kirista, ya ce kul aka sake kiransa da Matthew

-Obasanjo yace zai sa kafan wando daya da duk wanda ya sake kiran sa Matthew

-Asalin mai sunan a litafin Bible wani sakaran mai karban haraji ne – Obasanjo

-Iyaye na sun rada min sunan ne domin nuna cewa dan da suka haifa kirista ne, inji Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi watsi da daya daga cikin sunayensa wato – Matthew, ya ci gaba da cewa duk wanda ya sake kiran sa Mathew zai gamu da “jan idon” sa.

Obasanjo yayi bayani cewa dalilin da yasa yayi watsi da sunnan shine asalin mai sunnan a cikin litafin Bible mai karban haraji ne, kuma shi baya karban haraji.

Obasanjo ya nesanta kansa da sunansa na kirista, ya ce kul aka sake kiransa da Matthew

Obasanjo ya nesanta kansa da sunansa na kirista, ya ce kul aka sake kiransa da Matthew

Tsohon shugaban yace sunayen da yake son a kira shi suna Olusegun Okikiola Aremu tunda wadannan sunayen suna da ma’anoni masu kyau a gargajiyance.

KUMA KU KARANTA: Abin tsoro: Yan sanda sun cafke mutane uku da kokon kan dan-adam

Obasanjo ya bada wannan gargadin ne a wata taro da Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya suka yi a babban birnin Najeriya Abuja.

Kamar yadda tsohon shugaban kasan ya fada, “A lokacin da aka haife ni, al’adar mutanen mu shine bayan kwana bakwai, za’a rada ma yaro suna, kuma domin a nuna ma mutane cewa gidan ku kirista ne za’a rada ma yaron suna ne irin na kabilar Hebrew da muka karanta labarin su a Bible.

Iyaye na sunyi shawara kuma suka rada min suna Matthew, amma bayan na girma sai na fara tambayan ma’anan sunan.

“Ma’anar kawai na iya gano wa shine asalin mai sunan Matthew a cikin Bible mai karban haraji ne, kuma har ila yau sakarai ne. duk wanda baya son musa kafan wando daya dashi ya daina kira na Matthew

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel