Bayan Osinbajo ka ji wadanda su ka ga Buhari a Landan

Bayan Osinbajo ka ji wadanda su ka ga Buhari a Landan

- Mun bi diddigi mun gano wasu daga cikin wadanda su ka iya ganawa da Buhari

- Tun bayan tafiyar Shugaban kasa Buhari babu wanda ya san halin da yake ciki

- Sai dai Matar sa da Mukadashin sa sun samu ganawa da shi a Birnin Landan

Mun bi diddigi daga Jaridu irin su The Nation mun gano wasu hala kadan daga cikin wadanda su ka iya ganawa da Shugaba Buhari tun bayan fitar sa Landan.

Mutane 5 da su ka kai wa Shugaba Buhari ziyara a Landan

Kwanaki da 'Yan Majalisa su kai ziyara ga Shugaba Buhari a Landan

1. Mukaddashin Shugaban kasa

Kun san cewa Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ma bayyana yadda su kayi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Landan inda su ka hadu na fiye da awa guda a daren Laraba.

2. Uwargidan sa Aisha Buhari

Hajiya Aisha Buhari ta kai ziyara Landan kusan ba sau daya ba ma inda ta gana da Mijin na ta kuma ta kira ‘Ya Najeriya su cigaba da addu’a.

Mutane 5 da su ka kai wa Shugaba Buhari ziyara a Landan

Uwargidar Shugaba Buhari ta kai masa ziyara

KU KARANTA: Bukola Sarki ya gagara ganin Shugaba Buhari

Mutane 5 da su ka kai wa Shugaba Buhari ziyara a Landan

Lokacin da Shugaba Buhari zai tafi Landan

3. Shugaban Hukumar DSS

Mallam Lawal Daura wanda shi ne Shugaban Hukuar DSS da ke kula da kare Shugaban kasar ya samu ganin Shugaban kasar.

4. Ministan Ilmin Najeriya

Ministan Ilmi na kasa Malam Adamu Adamu yana cikin wadanda su ka samu ganin Shugaba Buhari tun bayan tafiyar sa. Alakar sa dai da Shugaba Buhari ba yau ta fara ba.

5. Ministan Shari’a na kasa

Bayan Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu mun ji cewa Abubakar Malami wanda yake na hannun dama kuma Ministan shari’a ya samu ganin Shugaban kasa Buhari kwanaki a Landan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me Yan Najeriya ke fada game da Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel