Jam'iyyar PDP ta kira wani gagarumin taro da gaggawa

Jam'iyyar PDP ta kira wani gagarumin taro da gaggawa

- Jam'iyyar PDP ta kira wani taron gangami babu wata-wata a gobe

- Makon jiya ne Kotun koli da yanke hukunci game da rikicin Jam'iyyar

- Gobe za ayi wannan babban taro a babban Ofishin Jam'iyyar a Abuja

Jim kadan bayan Jam'iyyar PDP ta shawo kan karshen rikicin ta sai ga shi an kira wani babban taro na manyan 'Yan Jam'iyyar domin shawo kan yadda Jam'iyyar adawar za ta cigaba.

Jam'iyyar PDP ta kira wani gagarumin taro da gaggawa

PDP ta kira taro na musamman gobe

Kamar yadda Shugabannin Jam'iyyar su ka bayyana za ayi taron Shugabannin Jam'iyyar ne da sauran masu fada aji a Jam'iyyar a gobe Litinin 17 ga wannan Wata a Abuja. Ana gayyatar kaf tsofaffin Ministoci da ‘Yan Majalisa na Jam’yyar.

KU KARANTA: Ana nema a nada Magajin Shugaba Buhari

Jam'iyyar PDP ta kira wani gagarumin taro da gaggawa

Shugaban Jam'iyyar PDP Ahmed Makarfi

Za dai a zauna ne da karfe 11:00 na safe da kuma karfe 2:00 na rana a babban Ofishin na Wadata Plaza a layin Michael Okpara na Unguwar Wuse Zone 5 kamar yadda Sakataren Jam'iyyar Ben Obi da Ambasada Aminu Wali ya sanar.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff yace ba shakka Jam’iyyar ta koma hannun manyan barayin kasar bayan da Kotun kolin kasar ta karbe shugabancin Jam’iyyar daga hannun sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najeriya sun gaji da Buhari kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel