Yan bindiga sun kashe makiyaya hudu a kudancin Kaduna

Yan bindiga sun kashe makiyaya hudu a kudancin Kaduna

- Anyi awon gaba da yan fulan biyu

-Miyyeti Allah tayi kira da mabiyanta da kada su dauki doka a hanun su

-Yansanda ba su ce komai ba game da abun da ya faru

Yan bindiga sun kashe makiyaya yan fulani guda hudu a karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna.

Har ila yau hukumar yan sanda basu ce komai game da abun da auku ba.

Sakataren kungiyan makiyayan Najeriya na Miyyeti Allah, Abdullahi Ibrahim ya fada ma manema labarai a ranar Asabar cewa bayan aika-aikan da yan bindigan sukayi sunyi awon gaba da yan fulan guda biyu.

Yan bindiga sun kashe makiyaya hudu a kudancin Kaduna

Yan bindiga sun kashe makiyaya hudu a kudancin Kaduna

Ya kuma kara dacewa yan bindiga wa yanda har ila yau ba a san ko su waye ba sun kara kai hari unguwan Tsohon Dimshi da ke karamar hukuman Chikun na jihar in da suka kara da rusa musu gidaje.

KU KARANTA: Saraki ya gagara ganin Buhari a Landan

A yayin da yake bayyana abun da yafaru cikin fushi da bakin ciki, Sakataren Miyyeti Allah yana kira da mabiyansa da su yi hakuri kada su dauki doka a hanun su , su bar hukuma tayi aikin ta wajen kama wa yanda suka aikata ta’adancin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana son bamu shawara ko aiko mana da labari, aika wannan akwaiti labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel