Kungiyar yan jarida ta kasa ta yi wa Gwamna El-rufai kakkausan gargadi

Kungiyar yan jarida ta kasa ta yi wa Gwamna El-rufai kakkausan gargadi

Kungiyar yan jarida ta kasa watau Nigerian Union of Journalist (NUJ) a turance tayi wani zama na musamman a ranar Alhamis din da ta gabata inda kuma ta gargadi Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-rufai na jihar Kaduna.

Babban sakataren kungiyar na Kasa Shu'aibu Leman ya bayyana hakan bayan tashi taron nasu da suka gudanar a sakariyar su dake a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Kungiyar yan jarida ta kasa ta yi wa Gwamna El-rufai kakkausan gargadi

Kungiyar yan jarida ta kasa ta yi wa Gwamna El-rufai kakkausan gargadi

NAIJ.com ta samu cewa wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnatin jihar ta shigar da kara suna tuhumar wani dan jarida mai suna Binniyat kan zargin rubuta labarin karya ga Gwamnan.

Haka ma sannan kuma sai kungiyar ta NUJ ta gargadi gwamna El-Rufai cewa shine zasu nema idan har wani abu ya sami Binniyat.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel