Har yanzu ina mamakin yadda za'a dauki jam'iyya mai martaba a ba barayi - Modu Shariff

Har yanzu ina mamakin yadda za'a dauki jam'iyya mai martaba a ba barayi - Modu Shariff

Kawo yanzu dai tuni tsohon shugaban jam'iyyar PDP mai adawa wanda kotun koli ta kora ya tattara yanasa-yanasa ya fice daga sakatariyar jam'iyyar da akeyi wa lakabi da Wadata plaza a cikin birnin Abuja.

Bayan da ya fice din kuma mai magana da yawun bangaren nasa wanda kotun ta kora mai suna Bernard Mikko ya fitar da sanarwa yana mai nuna kaduwa da kuma mamakin yadda akayi kotun ta dauki ragamar jam'iyyar ta ba mutanen da ya kira 'barayin gwamnati'.

Har yanzu ina mamakin yadda za'a dauki jam'iyya mai martaba a ba barayi - Modu Shariff

Har yanzu ina mamakin yadda za'a dauki jam'iyya mai martaba a ba barayi - Modu Shariff

NAIJ.com ta samu cewa a cikin sanarwar ya ce: ”Mun karbi hukuncin kotun kolin kan shugabancin jam’iyar PDP cikin kaduwa. Duk da cewa muna jiran cikakken hukuncin kotun a rubuce daga hannun lauyoyin mu inda zasu yimana cikakken bayanin hukuncin."

An dai ruwaito cewa motocin yan sanda ne aka turo suka kwashe kayayyakin tsohon korarren shugaban na PDP daga sakatariyar jam'iyyar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel