Tarihi zai maimaita kansa? Kamanceceniya 3 da rashin lafiyar Buhari keyi da ta marigari Ummaru Musa

Tarihi zai maimaita kansa? Kamanceceniya 3 da rashin lafiyar Buhari keyi da ta marigari Ummaru Musa

Ya zuwa yanzu hankalin yan Najeriya gaba daya ya raja'a zuwa ga ganin halin da shugaba Buhari yake a yanzu wanda ya shafe fiye da watanni biyu yanzu haka yana jinya a birnin Landan dake a kasar Birtaniya.

Wannan dai yasa masu sharhi da dama fara shakku a kan ko tarihi ne ke shirin maimaita kansa a kan shugaban na Najeriya ganin cewa da haka ne shima marigayi Ummaru Musa Yar'aduwa ya fara?

NAIJ.com ta tattaro ma masu karatun mu hanyoyi 3 da rashin lafiyar ta Buhari tayi kamanceceniya da ta Ummaru .

1. Rashin bayyana a bainar jama'a:

Kamar yadda aka hana yan Najeriya ganin marigayi shugaba Yar'adua, hakan ma har yanzu makusantan shugaba Buhari sunki bari yan kasa su ganshi.

2. Kiraye-kirayen murabus:

Tarihi zai maimaita kansa? Kamanceceniya 3 da rashin lafiyar Buhari keyi da ta marigari Ummaru Musa

Tarihi zai maimaita kansa? Kamanceceniya 3 da rashin lafiyar Buhari keyi da ta marigari Ummaru Musa

Shima a lokacin da marigayi Ummaru Musa yana tasa jinyar, wasu da yada daga manyan yan Najeriya ciki kuwa hadda shugaba Buharin sunyi ta kira yayi murabus. Yanzu ma mutane irin su Fayose tuni sun fara kira da Buhari yayi murabus.

3. Rashin sanin yaushe Buhari zai dawo:

Kawo yanzu dai ba mahalukin da zai iya fada maka takamaiman ranar da shugaba Buharin zai dawo ganin cewa ko mataimakin sa ma bai sani ba.

Haka akayi shima lokacin marigayi Ummaru Musa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel