Wani gwamna ya ce shine zai gaji Buhari a zaben shekarar 2019

Wani gwamna ya ce shine zai gaji Buhari a zaben shekarar 2019

- Gwamna Fayose ya jaddada cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019

- Fayose ya ce ya yi imani cewa zai ci galaba a kan shugaba Buhari a 2019

- Gwamnan na cewa gwamnatin jam’iyyar APC ba za ta koma Villa ba

Shugaban gwamnonin jam'iyyar ta PDP, Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya sake jaddada cewa babu abin da zai hana shi zama shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2019.

Fayose ya shaidawa manema labarai a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar juma’a, 14 ga watan Yuli cewa jam’iyyar PDP za ta fara wayar da kan mutanen yankunan karkara kafin zaben 2019 ta gabato.

Fayose ya ce: "Ina so in gaya muku cewa jam’iyyar APC ba za ta koma Villa a 2019 ba. Za mu kayar da Buhari da Osinbajo gaba daya”.

Wani gwamna ya ce shine zai gaji Buhari a zaben shekarar 2019

Ayodele Fayose na jihar Ekiti

A Lokacin da ‘yan jarida suka tambaye sa game da takarar shugabancin kasar, Fayose ya ce har yanzu yana kan bakansa.

KU KARANTA: Nayi niyyar kona katin jami'iyya ta idan Sheriff yayi nasara a kotu - Fayose

A karshen makon nan ne gwamna Fayose ya ce zai saki wasu hotunan shugaba Buhari wanda zai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shugaban na cikin wani mummunan rashin lafiya.

Idan dai baku manta ba NAIJ.com ta kawo muku rahoto cewa shugaban kungiyar matasan arewa AYF, Gambo Gujungu ya zargi shugabannin yankin kudu maso yammacin kasar da amfani da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon ministan, Femi Fani-Kayode da su gurgunta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da kuma jawo tsabani tsakanin ‘yan Najeriya da yankin Arewacin kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel