Matar Farfesa Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya

Matar Farfesa Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya

- Matar Farfesa Yemi Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya

- Mukaddashin Shugaban kasar ya taya ta murna cikin dare

- Farfesa Osinbajo yace yana alfahari da matar ta sa Dolapo

A safiyar yau ne Matar Farfesa Yemi Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya da haihuwa. Haka kuma Mijin na ta ya dauki lokaci inda ya taya ta murar zagayowar wannan rana.

Matar Farfesa Osinbajo ta cika shekaru 50 a Duniya

Hotton Iyalin Farfesa Osinbajo daga Fadar shugaban kasa

Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya taya Uwar ‘ya ‘yan ta sa 3 murna na musamman inda ya kawo mata ‘dan kek cikin dare lokacin yayin da ba tayi tsammani ba. Osinbajo yake cewa ita ce fika-fikan sa da yake tinkaho da su.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ya nemi a gyara kasar nan

Shekaru fiye da 27 kenan da auren Farfesa Osinbajo da Dolapo wanda jika ce ta tsohon Firimiya na Kasar Yarbawa Marigayi Cif Obafemi Awolowo. Matar Shugaban kasa watau Aisha Buhari ta taya kawar ta murnar wannan rana.

Kun ji cewa Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya kara jaddada cewa shi zai karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo. Fayose yace da Shugaba Buhari da Osinbajo duka za su bar Fadar Shugaban kasa a zaben na 2019 mai zuwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An ga hoto Yesu a wai coci?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel