Kamfanin mai na NNPC ya fidda sabbin dabarun kama barayin mai

Kamfanin mai na NNPC ya fidda sabbin dabarun kama barayin mai

- Kamfanin mai na NNPC ya sami dabarar hana satar danyen mai a kai a sayar a kasashen waje

- A yanzu dai ana sace wa Najeriya mai da yawa

- Barnar satar tana kuma kawo asara da kuma fashe-fashen bututun mai

Kamfanin mai na NNPC ya ce ya sami wata sabuwar dabarar kimiyya da zayyi amani da ita don ganowa da magance matsalar sace-sacen mai da ake yi wa kasa tare da barnar kudi da bata muhalli.

A karkashin shirin dai kamfanin zai zuba ido kan mayukan da ake sha a kasashen duniya, inda za'a gano inda aake shan man da aka sata a Najeriya aka fitar ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin mai na NNPC ya fidda sabbin dabarun kama barayin mai

Kamfanin mai na NNPC ya fidda sabbin dabarun kama barayin mai

Satar mai dai ta ame wa wasu marasa aikin yi hanyar samun kudi cikin gaggawa, inda suke fashe bututan mai su cika gangunansu su tace man, ko kuma su sayar a wasu kasashen da ke da bukatar mai mai araha.

A yanzu dai fasahar zata karanta samfurin man Najeriya ta saka a kwamfayuta sai a bi duk mai da aka san na sata ne a kashen waje domin ganewa ko na Najeriyar ne.

DUBA WANNAN: Fani Kayode yayi wa Arewa raddi

Manajan Kamfanin bangaren fasaha Abiola FAlowo ne tayi wannan bayani, a Fatakwal yayin lacca kan yadda za'a magance satar danyen man da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.

A shekarar 2014 dai Najeriya ce kasa da tafi kowa yawan satar mai a duniya, duk ka hada da Iraki da Libiya wadda 'yan ta'adda suka mamaye a wannan lokaci.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel