Jam'iyyar PDP ta koma hannun barayi, rainin wayo ne ace wai an yaffe mana, inji Sheriff

Jam'iyyar PDP ta koma hannun barayi, rainin wayo ne ace wai an yaffe mana, inji Sheriff

- PDP ta fada ha'ula'i a hannun Ahmed Makarfi

- Bani da wani shafi nawa a tuwita

- Rainin wayo ne a ce an yafe mana

Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon shugaban bangare na jam'iyyar PDP, ya musanta cewa ya taya bangaren Ahmed Makarfi murnar darewa kan karagar jam'iyyar PDP, inda yace shi baya ma da wani shafi na tuwita balle har yayi amani dashi, kamar yadda wasu kaaen yada labarai suka ruwaito.

Jam'iyyar PDP ta koma hannun barayi, inji Sheriff

Jam'iyyar PDP ta koma hannun barayi, inji Sheriff

Ali Sheriff, yace sun kadu matuka da hukuncin da kotun kolin ta yanke, sannan ya ce rainin wayo ne ma ace wai an musu afuwa kan jayayya da suka yi da shugabancin Ahmed Makarfi.

A ta bakin kakakinsa, Mr. Bernard Mikko, yace 'ai ba wai haka nan siddaran muka shiga Wadata Plaza ba kamar wasu haramtattun shuwagabanni, zabe akayi muka shiga muka ci, to don me za'a ce wai an yafe mana kamar munyi ba daidai ba?'

An dai jiyo bangaren Ahmed Makarfi na cewa sun yi yaffiya ga bangaren Sherif din ne tun bayan da kotu ta mika musu ragamar jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Sarkin Kano yace in ya so zai iya samun makudan kudade daga kishingide

Kuma ma dai, kakakin na Ali Sheriff, yace abin takaici ne a ce jam'iyyar su ta PDP ta fada hannun wadanda suke da manyan kesa-kesai a kotunan kasar nan, kan badakala da cin hanci da rashawa da almundahana da kudaden gwamnati lokacin suna kan karagar mulki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel