Saraki ya gagara ganin Buhari a Birnin Landan

Saraki ya gagara ganin Buhari a Birnin Landan

- An shirya a da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki zai gana da Buhari a birnin Landan

- Ya dawo fanko ba tare da ya sami damar ganawa da shi ba

- Ana ganin wannan na da nasaba da yadda ake samun takun saka tsakanin majalisa da fadar gwamnati

A ziyarar da yake a Ingila, ta bikin yaye dalibai a makarantar da dansa ke ciki, a karshen makon nan, an sa rai Shugaban majalisar zai gana da shugaba Buhari a Abuja House, inda yake jinya, sai dai hakan bai samu ba inda Bukola Sarakin ya dawo gida ba tare da ya sami ganinsa ba.

Saraki ya gagara ganin Buhari a Birnin Landan

Saraki ya gagara ganin Buhari a Birnin Landan

A cewar bayanai de daga bangaren majalisar, an sa rai bayan ganawa da Faresa Yemi Osinbajo, za'a kuma bi kadin ganawar da shima shugaban majalisar sai dai gashi hakan bai yiwu ba.

Takun saqa ya karu tsakanin majalisa da adar gwamnati tun bayan tafiyar shugaba Buhari asibiti jinya, batu da ya kai wai har ana so a dora shugaban majalisar a matsayin shugaban kasa yayin da Farfesa Osinbajo yayi bulaguro.

DUBA WANNAN: Fani Kayode ya sake caccakar samarin arewa

Batun tantance shugaban EFCC Magu, da ma batun daukaka kara zuwa kotu kan batun rashawa da cin hanci da gwamnati ta shigar kan shi shugaban majalisa duk dai ya kwaciba al'amarin gudanar da mulki cikin raha tsakanin gwamnatocin masu cin gashin kansu a tarayya.

A yanzu da, dawowar shugaba Buhari zata nuna ko gaba ta kullu a tsakanin gaggan 'yan siyasar ne, ko kuma kawai rashin sa'ar ganin shugaban Bukola Sarakin ya yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel