Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya nemi a sauya tsarin Najeriya

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya nemi a sauya tsarin Najeriya

- Atiku Abubakar ya kara kira ayi wa Najeriya garambawul

- Wazirin Adamawa yace hakane Jihohi za su kara karfi

- Jama’a na ta kira ayi wa Kasar garambawul domin a cigaba

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya nemi a sauya tsarin Najeriya domin Jihohin Kasar 36 su kara karfi fiye da yadda ake yanzu.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya nemi a sauya tsarin Najeriya

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi kira ayi wa Najeriya garambawul

Atiku Abubakar yace idan har aka sauya tsari kasar Jihohi za su kara dagewa wajen neman kudin shiga. Tsohon Mataimakin Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi game da batun raba kasar da hadin ka a Abuja.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya caccaki wasu Kiristoci

Wazirin na Adamawa yace dole fa a zauna a tattauna game da maganar yi wa kasar garambawul. A cewar sa haka zai kara karfi ga Jihohin kasar don kuwa a wannan tsari da ake tafiya da dama sun zama malalata.

Jama'a da dama a Najeriya dai yanzu su na kira a sauya tsarin kasar inda kowane Yanki zai kara karfi ya kuma rage dogaro da wani ko kuma Gwamnatin Tarayya. An dai dogara da man fetur din da ke Kudancin kasar ne.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da fafutukar Biyafara da Nnamdi Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel