An gano masu tallafawa kungiyoyin ‘yan daba a yankin Neja Delta

An gano masu tallafawa kungiyoyin ‘yan daba a yankin Neja Delta

- Rundunar sojojin Najeriya tace ta gano masu tallafawa wasu kungiyoyin ‘yan daba a jihar Ribas

- Wani basarake da dan majalisar wakilan Najeriya ne masu bada tallafin

- Babban hafsan sojoji ya ce gwamnati da kuma al'ummar nada muhimmanci ganin a samu zaman lafiya a jihar

Rundunar sojojin Najeriya tace ta gano masu tallafawa wasu kungiyoyin ‘yan daba mafi muni biyu a jihar Ribas.

A cewar babban kwamandan rundunar soja na 6 Division a Fatakwal, Manjo janar Enobong Udoh ya ce masu tallafawa ‘yan daba sun hada da dan majalisar wakilai da wani basarake a yankin al’ummar Ozoji da ke jihar Ribas. Wadannan shugabanin ke tallafawa ‘yan daba Ice Landers da Greenlanders fraternities a yankin Ahoada na jihar.

Udoh ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da wasu shugabanin sojojin kasar a karkashin jagorancin babban hafsan sojoji, Laftana janar Tukur Buratai da kuma sarakunan gargajiya a jihar.

Ya ce: "A Ahoada ta gabas, ina sane da matsalar da ake samu da ‘yan daba Icelanders da Greenlanders. Ina tabbatar maku cewa sarkin Ozochi ake zargi da tallafawa Greenlanders kuma dan majalisar wakilai ke tallafawa Icelanders".

KU KARANTA: Turnuku! Sojin ruwan Najeriya sun fatattaki barayin da suka so sace wani babban jirgin ruwa

" Amma na gayyaci duka mutane biyu da kuma mai ba gwamnan jihar shawarwari a kan rikice rikice”.

A nasa bangare, babban hafsan sojoji, Laftana janar Buratai ya ce sojoji zasu yi aiki tare da 'yan sanda da kuma sauran jami'an tsaro ko da yaushe domin samu zaunanniya zaman lafiya a jihar.

"Sarakunan gargajiya da gwamnati da kuma al'ummar nada muhimmanci ganin a samu zaman lafiya a jihar." A cewar Buratai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel