Abin tsoro: Yan sanda sun cafke mutane uku da kokon kan dan-adam

Abin tsoro: Yan sanda sun cafke mutane uku da kokon kan dan-adam

-An cafke wasu mutane da kokon kan da adam

-Wanda ake cafke sunce an zo da kokon kan ne daga kasar Kwatano

-Yan sanda suna cigaba da bincike domin wanzar da hukuncin da ya dace

Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun ka cafke wasu mutane uku bayan an same su da kokon-kai na dan-adam. Wannan sanarwan ya fito ne data bakin jami'i mai magana da yawun rundunar mai suna Mr Abinbola Oyeyemi, mutane ukun da aka kama sune; Saibu Papoola, Aliu Ajuroba da kuma Jimoh Ijiola.

Abin tsoro: Yan sanda sun cafke mutane uku da kokon kan dan-adam

Abin tsoro: Yan sanda sun cafke mutane uku da kokon kan dan-adam

Oyeyemi ya bayyana cewa an cafke wadanda ake zargin ne a yayin da jami'an rundunar aiki a unguwar Oyetoro ke kewaye a unguwar inda suka hadu da Papoola da Ajuroba akan babur dauke da jaka wanda basu yarda da ita ba.

KUMA KU KARANTA:

Bayan sun tsare su sun duba jakar, sai suka ga kokon-kan dan adam. Papoola da Ajuroba suka ce wani mutum mai suna Ijiola ne ya basu. Yan sandan suka tasa keyar su zuwa gidan Ijiola da ke unguwar Erinpa a karkashin jagorancin DPO Makinde Kayode inda ake cafke wanda ake zargin na uku wato Ijiola.

Daga bisani bincike ya nuna cewa an samo kokon kan ne daga kasar Kwatano domin yin amfani dashi ayi kudin tsafi. A yanzu dai, kwamishinan yan sandan jihar Ahmed Iliyasu ya bada umarnin mika wanda ake zargi zuwa ga yan sanda masu binciken manyan laifi (CID) domin karin bincike da guma hukunci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel