Sanata Shehu Sani ya caccaki wani shugaban Arewa, karanta...

Sanata Shehu Sani ya caccaki wani shugaban Arewa, karanta...

- Sanata Shehu Sani ya kalubalanci kalaman janar T.Y Danjuma kan gwamnatin shugaba Buhari

- Sani ya ce kalaman wasu dattijan kasar zai iya zai iya hada fitina

- Sanata Sani ya yi watsi da zargin cewa gwamnatin Buhari na kokarin musuluntar da Najeriya

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasar waje da basusukan gida, sanata Shehu Sani ya gaya wa janar T. Y. Danjuma mai ritaya cewa kalamansa zai iya hada fitina a Najeriya.

Sanatan ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da rahotanni da cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya na kokarin musuluntar da Najeriya.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Sani ya rubuta hakan ne a shafinsa ta Facebook a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli cewa irin wannan kalaman janar T. Y. Danjuma mai ritaya da kuma wasu dattawan kasar zai iya barazana ga wanzuwar Najeriya.

Sanata Shehu Sani ya caccaki wani shugaban Arewa, karanta...

Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya

Sani ya rubuta cewa: " Wannan rashin adalci ne ga shugaba Buhari cewa wani mutum ko kungiya za su iya zargi gwamnatinsa cewa yana da wani ajanda. Sauran batutuwan game da gwamnatinsa zai iya ko ba zai zama gaskiya ba, amma lalle shugaba Buhari ma mai tsattsauran ra'ayi bane . Idan akwai wata makarkashiya a gwamnatin nan ina daga cikin wadanda za su fara tada kayar baya”.

KU KARANTA: Danjuma da wasu dattawan kirista sun yi Allah wadai da gwamnatin Buhari

Ya ce: "Kalaman dattijai na kirki ya kamata ya zama abin da zai haifar da zaman lafiya da hadin kan kasa kuma tsananta rikici ba”.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel