Shugaban kasa: Ni zan gaji Shugaba Buhari-Gwamna Fayose

Shugaban kasa: Ni zan gaji Shugaba Buhari-Gwamna Fayose

- Gwamna Fayose yace shi zai karbi mulki daga hannun Buhari

- Ba dai yau ne Gwamnan ya fara fadin irin wannan magana ba

- Gwamnan Jihar Ekitin yace a 2019 shi zai zama Shugaban kasa

Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya kara jaddada cewa shi zai karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2019.

Shugaban kasa: Ni zan gaji Shugaba Buhari-Gwamna Fayose

Fayose zai zama Shugaban kasa? Hoto daga Daily Post

Gwamnan dai ya saba fadin wannan magana, wannan karo yace yana so jama'a su yarda da abin da yake fada. Fayose yace da Shugaba Buhari da Osinbajo duka za su fatattaka daga Fadar Shugaban kasa a zaben na 2019 mai zuwa.

KU KARANTA: Osinbajo ya gana ne da Buhari na awa guda

Shugaban kasa: Ni zan gaji Shugaba Buhari-Gwamna Fayose

Gwamna Ayo Fayosezai zama Shugaban kasa bayan Buhari. Hoto daga AFP

Ayo Fayose yace bai ga dalilin da zai hana su buge Jam’iyyar APC wajen zaben ba. Fayose yace yanzu ya fara kokarin tattaro jama'a da za su mara masa baya a zaben da za ayi kamar yadda ya kudira.

Wani Matashi mai suna Adeyanju Deji da ke cikin manya a Jam'iyyar adawa ya soki Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da halin rashin lafiyar sa. Deji yace ya zama dole Muhammadu Buhari yayi wa 'Yan Najeriya halin da yake ciki ko ya bar mulkin Kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da shirin yi wa Najeriya garambawul

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel