Kungiyar MASSOB ta Neja-Delta tayi watsa-watsa da Matasan Arewa

Kungiyar MASSOB ta Neja-Delta tayi watsa-watsa da Matasan Arewa

- Kungiyar MASSOB ta Neja-Delta tace Matasan Arewa ba su da saiti

- MASSOB ta soki Kungiyar Arewa game da maganar Biyafara

- 'Yan Arewa su ka fara takulo wannan magana kwanan nan

Kungiyar MASSOB ta Neja-Delta ta soki wata Kungiyar Matasan Arewa bisa kalaman da tayi na cewa Kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu tana cikin Kungiyoyin 'Yan ta'adda.

Kungiyar MASSOB ta Neja-Delta tayi watsa-watsa da Matasan Arewa

Biyafara: 'Yan Neja-Delta sun yi kaca-kaca da Kungiyar Arewa

MASSOB ta zargi Matasan Arewan da rashin saiti inda tace ba su san inda su ka dosa ba gaba daya. Kungiyar tace Matasan na Arewa ma dai sam ba su san ma'anar ta'addanci ba saboda karancin sani.

KU KARANTA: Ka da Shugaba Buhari ya sake ya tsaya takara-Soyinka

Kungiyar MASSOB ta Neja-Delta tayi watsa-watsa da Matasan Arewa

Hoton 'Yan Kungiyar Biyafara daga Jaridar Daily Post

Wani babban Dan Kungiyar na MASSOB Kwamared Edeson Samuel yayi wannan jawabi yace 'Yan Biyafara 'yanci su ke nema ba fitina su ka nufa ba don mafi yawan 'Yan Yankin Jahilai ne shiyasa su ka gaza gane wannan.

Wani Sarki na kasar Yarbawa watau Alafin na kasar Oyo ya nuna goyon bayan sa na ayi wa Najeriya garambawul idan ana so kasar nan ta cigaba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Irin kokarin da wani Gwamna yayi a Jihar sa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel