Shugaban NHIS da aka dakatar yace yana nan a kujerar sa

Shugaban NHIS da aka dakatar yace yana nan a kujerar sa

- Shugaban Hukumar NHIS da aka dakatar yace yana nan a kujerar sa

- Farfesa Usman Yusuf yace Shugaban kasa kadai ya isa ya cire shi

- Ministan lafiya ya umarci Shugaban Hukumar ya dakata daga aiki

Farfesa Usman Yusuf wanda shi ne Shugaban Hukumar NHIS ya fadawa Ministan lafiya na Kasa watau Farfesa Isaac Adewole cewa babu wanda ya isa cire sa daga kujerar sa sai Shugaban kasa.

Shugaban NHIS da aka dakatar yace yana nan a kujerar sa

Shugaban Hukumar NHIS Umar Yusuf

Umar Yusuf yayi facali da dakatar da shi da Ministan lafiya Isaac Adewole yayi na watanni uku bisa wasu zargi inda yace a jira a kamala binciken kafin a dauki mataki wanda Ministan bai da ita a dokar aiki.

KU KARANTA: An bayyana dadewar ganawar Buhari da Osinbajo

Shugaban NHIS da aka dakatar yace yana nan a kujerar sa

Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole

Farfesa Yusuf wanda asalin dan Jihar Katsina ne yace Sugaban kasa Buhari ya nada sa aikin nan na shekara 5 kuma shi kadai ya isa ya tunbuke sa ko ya dakatar da shi a tsarin dokar Hukumar ta NHIS.

Kwanaki Hukumar EFCC ta maka wani Umar Faruk da kamfanin sa a Kotu inda ake zargin sa da laifin karkatar da wasu kudin kwangila da aka ba shi a Jihar Kaduna amma yayi mursisi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Maganin sanyi a lokacin damina

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel