Arewa bata isa ta saka ni inyi shiru ba, su harbo in harba ne - Fani-Kayode

Arewa bata isa ta saka ni inyi shiru ba, su harbo in harba ne - Fani-Kayode

- An san Fani Kayode da karadi kan kabilanci da addinanci

- Yace Arewa bata isa ta saka yayi shiru kan danniya ba

- Ana zargin Ayo Fayose da FFK kan son tada hargitsi a kasa

A martani da ya fitar ta hannun hadiminsa, Jude Ndukwe, kan zargin da wasu samarin arewa suka yi masa da abokin sa na PDP Ayo Fayose, kan son tada yaki na kabilanci a kasar Najeriya, Fani Kayode tsohon Minista yace babu wanda ya isa ya hana su magana daga arewa.

Arewa bata isa ta saka ni inyi shiru ba, su harbo in harba ne - Fani-Kayode

Arewa bata isa ta saka ni inyi shiru ba, su harbo in harba ne - Fani-Kayode

'Sanarwa da wani daga cikin samarin arewa ya ffitar na wai hukuma ta kama mu ko ta tsawatar mana, bazai saka mu muyi shiru ba, arewa ta harba mu harba ne' inji sanarwas.

A yanzu dai an ma saba da jin maganganu masu zafi na fita tsakanin wasu daga kudancin kasar nan, wasu kuma daga arewar kasar nan, kan batutuwa da dama, wadanda suka hada da siyasa, da addinanci, da kabilanci da ma bangaranci.

Ana saka ran hakan zai kara zafafa kan duba da yadda ake kara fuskantar zabukan 2019, da ma kuma rashin laiya shugaba Buhari wadda ta hana samar da tabbas kan siyasar shi.

DUBA WANNAN: 2019: Soyinka ya shawarci shugaba Buhari kan takara

A dai sanarwar, FK ya ce samarin ba sa wakiltar sauran samarin arewa masu hankali, inda ya kira masu kiran a kame shi da cewa 'yan karadi ne da ake amani dasu domin siyasa kuma a yi wulli dasu in an cimma buri.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel