Nayi niyyar kona katin jami'iyya ta idan Sheriff yayi nasara a kotu - Fayose

Nayi niyyar kona katin jami'iyya ta idan Sheriff yayi nasara a kotu - Fayose

-Idan da Sheriff yayi nasara, zan kona kona tutar jami’iyya da katin shaida na a harabar kotu, inji Fayose

-Ba yadda za’ayi in ci gaba da zama a jami’iyyar da yan bogi ke shuganci – Fayose

-Buhari da Osinbanjo baza su kai labara ba a zaben 2019, inji Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose dai yana daya daga cikin manyan masu adawa da tsagin Ali Modu Sheriff a lokacin da jam’iyyar ke fuskantar rikicin shugabanci.

Bayan kotu ta tabbatar ma tsagin Senata Ahmed Makarfi da shugabancin jami’iyyar, Fayose ya bar Abuja ya koma jihar sa ta Ekiti cikin murna da farin ciki, bayan shigar sa garin Ado Ekiti, ya bada sanarwan cewa ya tafi kotu ne da turare wanda zai fesa akan katin shaidar jami’iyyar PDP da kuma tutar jami’iyyar sannan ya banka musu wuta.

Nayi niyyar kona katin jami'iyya ta idan Sheriff yayi nasara a kotu - Fayose

Nayi niyyar kona katin jami'iyya ta idan Sheriff yayi nasara a kotu - Fayose

Bazan taba iya zama a jami’iyya daya tare da yan bogi.” inji Fayose

Gwamnan ya cigaba da cewa, da wannan nasaran da suka samu, shugaba Buhari da mataimakin sa Osinbanjo baza su kai labara ba a shekara ta 2019 domin zasu zage damtse wajen farfado da jami’iyyar tasu da PDP.

DUBA WANNAN: Buhari ya hakura a 2019, inji Wole Soyinka

Na tafi kotu da turare na wand azan fesa akan katin shaidar jami’iyya ta da tutar jami’iyyan a cikin harabar kotun idan da Sheriff yayi nasara, dalilin da yasa na tafi korun kenan.”

Yace daga yanzu jami’iyyar zata fara gamgami domin hada kan mutane tun daga mataki na kasa domin yadda za’a kada Shugaba Buhari da mataimakin sa a zabe mai zuwa.

Ina son in shaida muku cewa Buhari da Osinbanjo baza su koma kujerar mulki ba a shekara ta 2019, zamu tumbuke su gaba daya.” inji shi

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu
NAIJ.com
Mailfire view pixel