Mabarata zasu fara biyan haraji - Gwamnatin tarayya

Mabarata zasu fara biyan haraji - Gwamnatin tarayya

-Gwamnatin tarayya tayi kira da duk yan kasa da su dage wurin biyan harajin su

-Gwamnatin tace babu wani dan kasa da za’a dauke masa nauyin biyan harajin, harda wanda suka riki bara a matsayin sana’a

-Gwamnatin tarayyar tace za’a fara bincike akan wanda basa biyan harajin

Ministan kudi na Najeriya, Umargida Kemi Adeosun tace zaman kasan nan zai gagari mara sa biyan haraji nan ba da dade wa ba. Ta bada wannan sanarwan ne a wata lekca ta da bada a Makarantar koyan kasuwanci na PWC a Legas.

Ta ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta dauki hayar kwararu a harkan binciko kadarori na kampanoni da mutane masu zaman kansu domin gano ko suna biyan harajin da ya dace. Ministan tace duk wanda aka samu da laifin kin biyan harajin zai fuskanci fushin hukuma.

Mabarata zasu fara biyan harji - Gwamnatin tarayya

Mabarata zasu fara biyan harji - Gwamnatin tarayya

“Muna aiki da bayanai kamar lambar tatancewa na banki wato (BVN), bayanan kayayakin da mutane suka mallaka, bayanan mallakan kampanoni da dai sauransu. Ta wannan hanyan ne zamu gane adadin harajin da mutane da kampanoni suke biya.

DUBA WANNAN: Buhari ya hakura da takara a 2019 inji Wole Soyinka

Zamu duba sakamakon binciken da muka samu da kuma kudi ko kaddarori da mutane suka mallaka domin mu gane idan suna biyan harajin da ya dace amma muna kira da jama’a da su rika biyan harajin nasu ba tare da an takura musu ba.

“Idan mutum yayi rajistan mota mai tsada sosai, wannan ya nuna yana da kudi. Misali idan kayi rajistan Marsandi kirar E-Class amma kana biyan harajin N100,000 kawai, wannan abin dubawa ne, abubuwan da mutane suka mallaka ne zai nuna mana irin harajin da ya kamata su biya.”

Har illa yau, tace babu wani dan kasa da aka dauke ma haraji domin wasu mabaratan suna samun miliyoyin naira. Gwamnati zata duba yadda suke rayuwarsu sannan a sa musu harajin da ya dace da su.

Har kudin da aka samu ta hanyar bara ma ana biya masa haraji. Ya kamata ka biya haraji koda bar ace sana’ar ka.” inji Ministan kudin.

Gwamnati ta ba wata kampanin Ingila mai suna Kroll aikin binciko kadarorin da yan Najeriya suka mallaka a gida da ma kasashen waje.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel