Gwamna El-Rufai ya kere sa’a, ya samu lambar yabo a Abuja (KARANTA)

Gwamna El-Rufai ya kere sa’a, ya samu lambar yabo a Abuja (KARANTA)

Jihar Kaduna ta samu jinjina da yabo a matsayin jihar data fi kowacce saukin dabbaka kasuwanci a duk fadin Najeriya daga kamfanin jaridar Business Day.

An karrama jihar ce ta hannun gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai a wata kasaitacciyar bikin karramawa da jaridar ta shirya a babban dakin taro na Transcorp Hilton dake Abuja.

KU KARANTA: Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

Taron daya gudana a ranar 13 ga watan Yulio ya samu halartan manyan baki da suka hada da gwamnonin kasar nan, irin su Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamna Simon Lalong, Gwamna Okezie Ikpeazu da sauran manyan baki.

Gwamna El-Rufai ya kere sa’a, ya samu lambar yabo a Abuja (KARANTA)

Gwamna El-Rufai

NAIJ.com ta ruwaito an yaba ma kokarin da gwamna El-Rufai keyi wajen ganin jihar Kaduna ta zamo masauki na farko ga masu zuba jari daga dukkanin fadin duniya.

Gwamna El-Rufai ya kere sa’a, ya samu lambar yabo a Abuja (KARANTA)

Gwamna El-Rufai tare da gwamnoni

Gwamna El-Rufai ya samu rakiyar matarsa da kuma mashawwarcinsa akan harkokin siyasa, Uba Sani.

Gwamna El-Rufai ya kere sa’a, ya samu lambar yabo a Abuja (KARANTA)

Gwamna El-Rufai tare da Uba Sani da Ganduje

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel