kungiyar matasan arewa na zargin shugabanin Yarabawa da zagon kasa ga gwamnatin Buhari

kungiyar matasan arewa na zargin shugabanin Yarabawa da zagon kasa ga gwamnatin Buhari

- Shugaban kungiyar matasan arewa ya ce wasu shugabanin Yarabawa na zagon kasa ga gwamnatin Buhari

-Shugaban ya ce yana cikin matasan arewa da suka gana da shugaba Buhari a Landan

- Gujungu ya bukaci Fayosa da ya fito da hotunan shugaba Buhari da ya yi alkawari

Shugaban kungiyar matasan arewa wato Arewa Youth Forum, AYF, Gambo Gujungu ya zargi shugabannin yankin kudu maso yammacin kasar da amfani da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon ministan, Femi Fani-Kayode da su gurgunta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da kuma jawo tsabani tsakanin ‘yan Najeriya da yankin Arewacin kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Gujungu ya yi wannan magana ne yayin da yake mayar da martani ga kalaman gwamna Fayose cewa zai saki wasu hotunan shugaba Buhari wanda zai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shugaban na cikin wani mummunan rashin lafiya.

A lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Abuja, shugaban kungiyar matasan ya bayyana ikirarin gwamnan a matsayin wani babban qarya, Gujungu ya jaddada cewa Buhari zai dawo kasar a kwanaki masu zuwa.

kungiyar matasan arewa na zargin shugabanin Yarabawa da zagon kasa ga gwamnatin Buhari

Arewa Youth Forum, AYF

KU KARANTA: Osinbajo ya gana da Buhari na tsawon awa 1 ba minti 5 ba – Fadar shugaban kasa

Gujungu bayyana cewa yana cikin tawagar kungiyar matasan da suka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan, ya kara da cewa shugaba Buhari zai koma bayan kammala wasu gwaje gwaje na yau da kullum.

Shugaban matasan ya gargadi yankin kudu maso yammacin kasar da su daina wasa da hadin kai ‘yan Najeriya domin samun zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel