Assha! Yan Najeriya 97 suka rasa ransu a kasar Kamaru

Assha! Yan Najeriya 97 suka rasa ransu a kasar Kamaru

Rahotannin masu sosa zuciya da muke samu na nuni da cewa kimanin yan Najeriya 97 ne suka rasa rayukan su a tsibirin nan na Bakassi dake tsakanin kasar Najeriya da kuma makwafciya Kamaru.

Yan Najeriya dake zaune a can yankin dai sun koka a kan yadda sukace sojoji da jami'an tsaron kasar suke muzguna musu ta hanyar bi gida-gida suna tilasta masu bada kudin da basu san da su ba.

Assha! Yan Najeriya 97 suka rasa ransu a kasar Kamaru

Assha! Yan Najeriya 97 suka rasa ransu a kasar Kamaru

NAIJ.com ta samu labarin cewa har ilayau mazauna yankin sun bayyana cewa jami'an tsaron kuma sukan harbe duka wanda bai bada kudin ba ba tare da jin ba'asi ba.

A nata bangaren, Gwamnatin Najeriya tuni ma'aikatar harkokin wajen ta ta bukaci jakadan kasar ta Kamaru ya yi mata bayani game da rahotannin cin zarafin 'yan Najeriyan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel