Zaben 2019: Sule Lamido yayi magana tun bayan nasarar da Makarfi ya samu a kotun Allah-ya-isa

Zaben 2019: Sule Lamido yayi magana tun bayan nasarar da Makarfi ya samu a kotun Allah-ya-isa

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa kuma jagora a jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Sule Lamido yayi wata magana mai jan hankali tun bayan da kotun koli taba bangaren Ahmad Makarfi gaskiya game da shugabancin jam'iyyar PDP a farkon satin nan.

Sule Lamido yace yanzu dai ba wani lokaci ne na jayayya ba ko ci gaba da fada amma lokaci ne da ya kamata jam'iyyar ta PDP ta fara shirin dinke barakar dake a cikin ta.

Zaben 2019: Sule Lamido yayi magana tun bayan nasarar da Makarfi ya samu a kotun Allah-ya-isa

Zaben 2019: Sule Lamido yayi magana tun bayan nasarar da Makarfi ya samu a kotun Allah-ya-isa

NAIJ.com dai ta samu labarin cewa a ranar Larabar da ta gabata ne kemanin kwanaki biyu kenan kotun koli dake zaman ta a Abuja ta bayyana kwamitin da Makarfi ke jagoranta a matsayin bangaren dake da hurumin shugabantar jam’iyar wacce ta sha kaye a zaben 2015.

Yan jam'iyyar dai musamman ma talakawan Najeriya yanzu sun zura ido suga ya jam'iyyar zata farfado daga baccin da tayi ganin cewa yanzu rikin nata ya kare sannan kuma zaben shekara ta 2019 na kara karatowa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel