Kishin-Kishin: Sarki Sanusi na shirin nada Kwankwaso dan masanin Kano

Kishin-Kishin: Sarki Sanusi na shirin nada Kwankwaso dan masanin Kano

Wasu labaran da muke samu daga majiyoyin mu daban-daban na nuni da cewa yanzu haka an dukufa an fara shirye-shiryen yadda za'a nada tsohon Gwamnan Kano kuma Sanatan jihar yankin ta na tsakiya watau Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin Dan Masanin Kano.

Majiyar ta mu har ila yau ta bayyana cewa tuni magoya bayan Gwamnan suka fara tattaunawa da masarautar jihar ta Kano don ganin yadda al'amarin zai wakana nan ba da dadewa ba.

Kishin-Kishin: Sarki Sanusi na shirin nada Kwankwaso dan masanin Kano

Kishin-Kishin: Sarki Sanusi na shirin nada Kwankwaso dan masanin Kano

NAIJ.com dai zata iya tuna cewa a farkon watan nan ne Dan Masanin Kanon marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule ya riga mu gidan gaskiya. Mutuwar dai ta Dan Masanin na Kano marigayi ta girgiza kasar gaba ya inda mutane da dama manyan su da kanana suka rika gabatar da addu'oin su gare shi.

Haka ma dai zamu iya tuna cewa cewa ma dai tsohon Gwamnan na Kano Kwankwaso shine ya nada mai martaba Sarkin Kano din Alhaji Sanusi Lamido Sanusi a shekarun baya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel