Yan siyasa sun gurbatad da kungiyar fafutukar kare hakin ma’aikatan Najeriya(NLC) - Wike

Yan siyasa sun gurbatad da kungiyar fafutukar kare hakin ma’aikatan Najeriya(NLC) - Wike

-Yan Najeriya na fushi da ku . saboda yanzu kun zama yan siyasa

-Babu mai iya Magana a kasar nan yanzu sabo da tsoron zuwa kurkuku

-Darajar kungiyar fafutukar neman yanci ma'aikata ya fadi warwas

Gwamnan jihar Rivas. Chief Nyesome Wike yace yan Najeriya na fushi da kungiyan fafutukar neman yanci ma’akata(NLC) saboda yan siyasa sun shige su.

Ya ce shigan da yan siyasa suka musu yasa basa iya aikin su yadda yakamata, wajen kare hakkin mara sa karfi a Najeriya.

Wike ya fadi haka a ranar Juma’a lokacin da shugaban NLC kwamarade Ayuba Wabba ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin Rivas. Yace Kungiya bata da karfi Kaman yadda aka santa a da saboda bangarancin da ke tsakanin su.

Yan siyasa sun gurbatad da kungiyar fafutukar kare hakin ma’aikata Najeriya(NLC)-Wike

Yan siyasa sun gurbatad da kungiyar fafutukar kare hakin ma’aikata Najeriya(NLC)-Wike

Gwamnan yace,: “ Yan Najeriya na fushi da ku . saboda yanzu kun zama yan siyasa. Karfin ku ya ragu ba Kaman da ba."

KU KARANTA: : Za'a daina biyan wasu kansiloli albashi

"Na tuna lokacin tsohon shugaban kasa Jonathan, da ku ka tsayar da kasan cak da yajin aiki saboda cire tallafin farashin man fetur. Amma yanzu an cire komai da komai kuma ba abun da ya faru.

Nayi matukar bakin ciki da darajar kungiya kwadago (NLC) ya fadi warwas, yanda idan suka kira yajin aiki dan kare hakin ma'aikata ba ya yiwuwa inji Wike.

Kun bar yan siyasa sun shige ku kuma sun samu nasarar raba kawunan ku yanzu kun zamo kungiya biyu."

Yayin da yake nuna ma kungiyar kwadagon goyon bayan sa, yayi kira da su tsaya akan aikin su bisa gaskiya da amana dan kare hakkin mara sa karfi.

Yace yanzu babu mai iya Magana a kasar sabo da tsoron zuwa kurkuku. Idan kayi Magana sai a turo maka hukuman bincike na EFCC. Idan baka son su kama ka sai ka canza sheka zuwa jam’iyyansu.

Akwai wani darekta na NDDC wanda dan jam’iyyar PDP ne, Hukuman EFCC ke tuhumar sa da aikata laifin zamba, amma yana canza sheka zuwa APC sai suka kyale shi.

Gwamnan ya tabbatar wa kungiya kwadagon da cewa zai cigaba da aiki da su dan warware duk wani matsala da ya shafi ma’aikatan jihar har wa’yanda suka yi ritaya.

Shuhgaban NLC kwamrade Ayuba Wabba ya yabi gwamnan wajen biyan albashi da fansho akan lokaci.

Kungiyan yan kasuwa sunce "nayi maka godiya akan biyan albashi da kake yi akan lokaci, dole mu shaida kuma mu yaba maka saboda mun ji labarin wasu jihohin da basu iya biyan albashi.

Ya kuma ja hankalin gwamnan jihar Rivas da ya duba matsalar wa’yanda suka ya ritaya bada jimawa ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel