Osinbajo ya gana da Buhari na tsawon awa 1 ba minti 5 ba – Fadar shugaban kasa

Osinbajo ya gana da Buhari na tsawon awa 1 ba minti 5 ba – Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta ce lallai ganawar da akayi tsakanin shugaban kasa Buhari da Osinbajo a Landan ya dauki tsawon awa guda

- Wata jaridar yanar gizo Sahara Reporters ta rahoto cewa Osinbajo ya dauki tsawon mintuna biyar ne kawai tare da Buhari a Landan

- Sahara Reporters ta kuma yi ikirarin cewa said a ya dauki Osinbajo tsawon mintuna 45 kafin na kewaye da shi su bari Osinbajo ya ga Buhari cikin sirri na tsawon mintuna biyar kawai

Fadar shugaban kasar Najeriya ta karyata rahoton kafar watsa labarai na cewa an bari mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan na tsawon mintuna biyar kawai.

NAIJ.com ta tattaro cewa mataimaki na musamman ga shugaban kasa Buhari a shafin zumunta, Bashir Ahmed a shafin twitter ya bayyana rahoton a matsayin karya domin a batar da jamaá.

Ahmad ya bayyana cewa a ranar 11 ga watan Yuli, shugaban kasa Buhari da mukaddashin shugaban kasa Osinbajo sun dauki tsawon saá daya suna ganawa mai kyau.

Osinbajo ya gana da Buhari na tsawon awa 1 ba minti 5 ba – Fadar shugaban kasa

Osinbajo ya gana da Buhari na tsawon awa 1 ba minti 5 ba inji Fadar shugaban kasa

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ya ci gidaje a Birnin Kebbi

Jaridar yanar gizo Sahara Reporters ta rahoto cewa Osinbajo ya dauki tsawon mintuna biyar ne kawai tare da Buhari a Landan. Ta yi ikirarin cewa ta samu rahoton ne daga wata majiya na fadar shugaban kasa wanda ya san abunda ya wakana a tsakanin shugabannin a “Abuja House”dake Landan.

Sahara Reporters ta kuma yi ikirarin cewa said a ya dauki Osinbajo tsawon mintuna 45 kafin na kewaye da shi su bari Osinbajo ya ga Buhari cikin sirri na tsawon mintuna biyar kawai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel