Injiniya ya ƙera ma Alhazai lemar zamani mai ɗauke da na’urar busa sanyi, AC (HOTO)

Injiniya ya ƙera ma Alhazai lemar zamani mai ɗauke da na’urar busa sanyi, AC (HOTO)

- Za'a fara amfani da na'urar sanyaya jiki a hajjin bana

- Wani Injiniya Mohammed Salegh ne ya kera wannan lemar

Wani masanin ilimin kimiyya da fasaha dan kasar Saudiya ya kera wata na’urar sanyaya jiki dake makale a jikin lema domin saukaka ma mahajjata zafin rana yayin da suke aikin hajjin bana.

Jaridar Saudi Gazette ce ta ruwaito wannan labari, inda tace injiniyan mai suna Mohammed Hamid Sayegh ya kudurci samar da wani abu daga iliminsa na kimiyya wanda zai taimaka ma alhazai, a haka ne ya samar da wannan lema.

KU KARANTA: Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

Mohammed yace “A yanzu haka ana cinikin wannan lema sosai da sosai, sakamakon alhazawa da dama dun fi bukatar amfani da lema a lokutan aikin Hajji.

Injiniya ya ƙera ma Alhazai lemar zamani mai ɗauke da na’urar busa sanyi, AC (HOTO)

Lemar ta musamman

"Lemar na amfani ne da hasken wutar lantarki, ko kuma ayi mata caji da wuta, ko a sanya mata batira, sa’annan ana iya makala masa goran ruwa, shi kuma ya fesa maka ruwan a jikinka don ka kara samun sauki.” Inji shi.

Injiniya ya ƙera ma Alhazai lemar zamani mai ɗauke da na’urar busa sanyi, AC (HOTO)

Lemar zamani

Majiyar NAIJ.com ta jiya Mohammed yana fadin ya kirkiri wannan lemar ne domin sauwwaka ma bakin Allah a yayin gabatar da ibadar aikin Hajji, sa’annan kuma yace farashin sa ba zai yi tsada ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda za'a magance sanyi da damuna:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel