Matsaloli 5 da jamíyyar PDP ka iya fuskanta duk da nasarar Makarfi

Matsaloli 5 da jamíyyar PDP ka iya fuskanta duk da nasarar Makarfi

Nasarar Ahmed Makarfi a kan Ali Modu Sheriff ya ba jamaá da dama mamaki kuma ya zo masu a bazata, wanda hakan ya sa kowa ke tofa albarkacin bakin sa a kan hukuncin da kotun kkoli ta yanke na ba bangaren Makarfi rinjaye kan Sheriff.

NAIJ.com ta duba wasu matsaloli da jamíyyar ta PDP ka iya fuskanta duk kuwa da cewa ragamarta ya koma hannun Sanata Ahmad Makarfi a yanzu.

1. Duk kuwa da cewan jamíyyar All Progressives Congress (APC) na cikin alhini, sannan jamaán Najeriya na cikin matsananciyar hali na tsadar rayuwa tun lokacin da APC ta amshi mulki, har gobe alúmman kasar na ganin cewa jamíyyar PDP ce sanadiyar sanya kasar a cikin halin da take a yanzu.

2. Har gobe a arewa, duk wadanda suka yi aiki a gwamnatin PDP sannan kuma ake masu kallon wadanda suka lamushe dukiyar kasar, sun gaza sakewa a cikin jamaá, saboda an mayar da su saniyar ware sai tsangwama ake masu.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun kuma kai hari a iyakar Kamaru da Najeriya, mutane 16 sun mutu

3. Ana ganin Ahmad Makarfi baida gogewa ta fannin siyasa a cikin sauran yan siyasar arewa, wanda nan ne sassalar sa. Ko a jihar Kaduna, baka jin sunan sa. Kuma sannan ga dukkan alamu na ciki-na-ciki tsakaninsa da abokin hamayarsa wato Sheriff.

4. Har wa yau a Arewa jamíyyar PDP ba ta da fikafikan yin faffaka sosai, kamar yadda ta ke yi a kudancin kasar nan. Babban jigon ta Namadi Sambo, shiru kake jin sa.

5. Idan ka debe tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, wanda a yanzu shi kadai ne za’a iya cewa ruhin PDP a Arewa, babu masu fitowa gaba-gadi su na kare jam’iyyar daga sara da sassakar da ‘yan APC ke yi mata. Dalili kenan masu lura da siyasar kasar nan ke cewa Lamido ne kadai zai iya fitowa ya daura banten kokawar yaki da APC har kila ya yi nasara a 2019.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel