Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

- Yansanda sun cafke masu garkuwa da mutane akan hanyar Abuja

- Dukkanin wadanda aka kama matasa ne hausawa daga jihohin Katsina da Kaduna

Biyo bayan yawaitan satar mutane a kan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja, babban sufeton yan sandan Najeriya, IGP Ibrahim K Idirs ya kaddamar da aiki na musamman akan hanyar domin magance matsalar.

Hakan ya sanya IG Idris zuba jami’an yansandan na musamman su 600 wadanda suke farautan barayin wurjanjan, inda a ranar 19 ga watan Yuni suka samu nasarar kama mutane takwas daga cikin masu garkuwan.

KU KARANTA: Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya karɓi baƙonci Tony Blair a Kaduna (HOTUNA)

Haka zalika a ranakun 8 da 9 ga watan Yuli jami’an Yansanda suka dira a mafakar masu garkuwan dake kauyukan Gwagwada, Kangimi da Katari, kuma sun samu nasarar kama su tare da kwato muggan makamai.

Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

Masu garkuwa da mutane

Wasu da aka kama sun hada Ibrahim Gurgu mai shekaru 45, Abdulazeez Idris mai shekaru 40, Shuaibu Ibrahim mai shekaru 29, Ibrahim Isiyaku mai shekaru 30, Usman Datti mai shekaru 30, Kabiru Musa mai shekaru 27 da Haruna Umar mai shekaru 24.

Yansanda sun kama masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (HOTUNA)

Masu garkuwa da mutane

Sai kuma makaman da aka kama sun hada da bindigar AK 47, Alburusai 30, kananan bindigu guda 2, layu da adduna 3, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabbin Sojojin Najeriya: Kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel