Shugaban NHIS yayi ko oho da umarnin ministan lafiya

Shugaban NHIS yayi ko oho da umarnin ministan lafiya

- Shugaban NHIS yayi watsi da umarnin Ministan lafiya

- Ana zargin Shugaban da rashawa

- Majalisar wakilai tace a yi kiranye ga shugaban

Shugaban NHIS (National Health Insurance Scheme) Usman Yusuf, yayi watsi da dakatarwar da ministan lafiya Isaac Adewole yayi masa a makon da ya gabata.

Ya rubuta wasika me kwanan wata 12/Yuli/2017 zuwa ga ministan na lafiya yana cewa; ba zai bi umarnin wannan dakatarwar da yayi masa ba ta ranar 6 ga watan Yuli na shekarar nan.

Mista Yusuf ya tabbatar da cewa wasikar ministan wadda take nuna cewa an dakatar da shi ta same shi, amma ba zai bi umarnin tab a don saboda wasu dalilai na shi guda biyar.

Shugaban NHIS yayi ko oho da da umarnin ministan lafiya

Shugaban NHIS yayi ko oho da da umarnin ministan lafiya

Shugaban me shekaru 54 a duniya ya karbi shugabancin wannan gidauniya a ranar 29 ga watan Yuli na shekarar 2016, sai dai ana zargin shugabancin na shi da barnar dukiya na babu dalili.

KU KARANTA: Dogara: An bukaci canja kundin tsarin mulki na 1999

Majalisar wakilai suna zargin Usman Yusuf da rashawa ta kimanin kudi Naira miliyan 292; wanda yace sun bata ne ta hanyar bada koyo ga wasu akan kiwon lafiya, wanda yayi hakan ne ba tare da zartarwa shugabannin sa ba.

Sanadiyar wannan laifin ne, majalisar ta bada umarni ga ministan domin yin kiranye akan shugaban na NHIS, wanda yace yayi kunen uwar shegu da wannan umarni. A dalilin wannan ne, wasu da dama daga cikin al’umma suke ganin abinda majalisar wakilai suka zartar bai dace ba.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel