Toh fa: Za a daina biyan wasu kansilolin arewa albashi

Toh fa: Za a daina biyan wasu kansilolin arewa albashi

- Gwamnatin jihar Filato tace za ta daina biyan kansilolin jihar albashi

- Yanzu haka alawus kawai ne kansilolin jihar Filato za su samu

- Gwamnan jihar ya ce shirin zai taimaka wajen rage kashe kudin gwamnatin

Gwamnatin jihar Filato ta sanar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli cewa za ta daina biyan kasilolin kananan hukumomi albashi, amma za a biya su kudin kowane zaman da suka yi a matsayin alawus.

Gwamna Simon Lalong ya bayyana hakan, inda kuma ya ce kansilolin za su zama kamar sau daya a cikin mako guda.

Gwamnan a lokacin da yake bayani a wani taron masu ruwa da tsaki na jama'iyyar mai mulki ta APC a Mangu, ya ce mataki na cikin matakan rage yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa ga shugabancin jihar a halin yanzu da kasar ke fuskantar koma bayan tattalin.

Toh fa: Za a daina biyan wasu kansilolin arewa albashi

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

NAIJ.com ta ruwaito cewa, gwamna Lalong ya shawarci masu ruwa da tsaki a kowane mazaba da su gabatar da wanda ya dace a matsayin wanda zai wakilce su.

KU KARANTA: Idan aka kaddamar da mutuwar Buhari, za’a daura El-Rufai a matsayin shugaban kasa – Fani-Kayode ya yi ikirari

Gwamnan ya ce wadanda za a nada shugabanin kanan hukumomi dole ne su kasance masu digiri, yayin da wadanda za a nada a matsayin kansiloli ya zama sun kammala karatun sakandare.

A lokacin da yake magana a madadin masu ruwa da tsaki, Sumaila Makama, daga mazabar Gindiri ya yaba wa gwamnan a kan ayyuka inganta rayuwar mutanen jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel