Dalilin da ya sa muka dakatar da kamfanin Atiku – Hadiza Bala Usman

Dalilin da ya sa muka dakatar da kamfanin Atiku – Hadiza Bala Usman

Shugabar hukumar tashoshin ruwan Najeriya wato NPA, Hadiza Bala Usman ta bayyana dalilan da suka sanya hukumar ta dakatar da kamfanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wato ‘Intels’.

A cewar ta sunyi hakan ne saboda su ba wasu kamfanoni dammar gudanar da ayyuka daidai da wanda kamfanin Intels ke aiwatar wa a tashoshin ruwa.

Ta bayyana hakan ne a zantawar da ta yi tare da jaridar Daily Trust.

Hadiza ta bayyana cewa ba wai sun yi hakan saboda su tozarta kamfanin Intels bane, a cewar ta sun yi hakan ne saboda kowa ya samu dammar shiga harkar ta dako da adana mai da kuma iskar gas a tashoshin kasar a maimakon a bari kamfanin Intels ta ci garenta ba babbaka.

Dalilin da ya sa muka dakatar da kamfanin Atiku – Hadiza Bala Usman

Hadiza Bala Usman ta bayyana dalilin dakatar da kamfanin Atiku

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ya ci gidaje a Birnin Kebbi

Da take amsa tambaya akan da zargi da ake yi na cewa hukumar ta yi haka ne saboda ta toshe hanyoyin samun kudin Atiku a kokarin ta na hana shi damar tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019, Hadiza ta ce wannan maganar ba komai bace face kage don ba haka suke nufi ba da dakatar da kamfanin mallakar Atiku ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel