CBN ta ware kudade Naira biliyan N10.4bn don tallafawa Manoma a jihar Borno

CBN ta ware kudade Naira biliyan N10.4bn don tallafawa Manoma a jihar Borno

- Kimanin manoma 20, 000 suka fara rajista a yayinda 5, 000 suka kammala tasu rajistar

- Manoman zasu karuda ababe kamar ; takin zamani, famfuna, kudade, kayan sifiri

Bankin Najeriya,(CBN) a yau ranar Juma'a ta bada sanarwar ta ware wa Jihar Borno kudi naira Biliyan goma da dugo hudu N10.45 don tallafawa harkar Noma a jihar

Mr Mahmud Nyako, Naya daga cikin Ma'aikatan bankin na CBN, ya sanarwa da manoma labarai a Maiduguri cewa an ware kudaden ne karkashin tsarin Anchor Borrowers Programme (ABP) wanda bankin kasa baki daya ya kirkiro.

CBN ta ware kudade Naira biliyan N10.4bn don tallafawa Manoma a jihar Borno

Noman Shinkafa a jihar Borno

NAIJ.com ta samo cewa tsarin ABP na daga mafi mahimmancin hanya da manufa da gwamnati ta dauka don tallafawa harkar noma wato Agriculture Transformation Agenda (ATA).

An kawo tsarin ne don karfafa manoma, da wayardasu a harkokin noman zamani.

Tsarin na gudanuwane tareda hadin guiwar gwamnonin jihohin Najeriya.

Nyako ya bayyana cewa manoma kimanin 40,000 wadanda ake tsammanin zasu noma shinkafa da wasu ababen noman bukata.

Kimanin manoma 20, 000 sukayi rajista ta farko a yanzu haka a yayinda 5, 000 suka kammala tasu rajistar.

KU KARANTA: Dangote zai zuba kudi kimanin biliyan $4.6 a harkar noma

“Tsare-tsaren zai gudanu ne ta gabobi biyu, Manoma 20,000 zasu dace da karon farko. a yayinda sauran zasu dace a daya karon"

Nyako ya kara da cewa manoman zasu karuda ababe kamar ; takin zamani, famfuna, kudade, kayan sifiri da sauransu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel